On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Aikin Gyaran Rijistar Zabe Da Sabunta Kati Ya Kankama A Masarautar Gaya – INEC Kano

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta samu nasarar yin gyara a katinan zabe sama da mutane dubu goma sha uku da dari biyu da talatin da shida na maza da mata da sabunta musu katin zabensu na din din din a karamar hukumar Gaya dake jihar Kano.

Shugaban Hukumar zaben mai kula da Karamar Hukumar ta Gaya Alhaji Yunusa Idris Barau shi ne ya bayyana hakan lokacin da yake karin haske game da irin nasarar da ofishin ya samu ga jami’in yada labarai na yankin Aminu Ahmad Rano.

Yunusa Idris Barau ya kara dacewa duk mutanen  da sukayi  rijista tun daga watan June shekara ta 2021 zuwa janairu na 2022 to Hukumar zaben ta kammala buga nasu katin zaben sai su ziyarci ofishin hukumar zaben dake yankunansu don karbar katin.

Ya kuma kara da cewa kashi na biyu na wadanda suka yi rijistar da hukumar daga janairu sha shida zuwa  talatin ga  wataN Yuni na  2022 zasu karbi nasu katin a watan oktoba na wannan shekara.

Barau ya mika godiyarsa ga dukkanin masu ruwa da tsaki Akan harkokin zabe na yankin tareda yin kira agaresu dasu cigaba da fadakar da al ummah cewa akwai katin zabe da za a iya karba a ofishin zabe na yankin sama da dubu hudu da dari daya da goma sha daya don haka duk wanda yayi rijista da Hukumar zaben to ya hanzarta zuwa don karbar katin nasa.