On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Aikin Hakar Man Fetur Na Kolmani Yana Da Tabbaci Ta Kowanne Bangare - Dr Tilde

Aikin hakowa da sarrafawa da kuma fitar da man Fetur da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar akan iyakokin jihohin Bauchi da Gombe, na cigaba da daukar hankali da samun martani daga masana da masu fashin baki da bibiyar al’amuran yau da kullum.

Dr Aliyu Tilde, wanda a yanzu shine kwamishinan ilimin Jihar Bauchi, ya jima yana sharhi akan tasirin wannan aiki ga yankin arewa maso gabashin Najeriya cikin raha da wasu hujoji da ya dogara da su yace lallai akwai tabbaci akan aikin.

Ga cikakken rubutun na Dr Tilde

Jiya mun halarci wajen kaddamar da shiri na aikin hakowa, sarrafawa da kuma sayar da man fetur na Kolmani. Waiwaiwai! Dad’i kashe ni, inji yan Hausa Film.

Ina farin cikin sanar da y’anuwana y’an Nijeriya cewa duk tsoron da muka nuna a baya game da dorewar abun an wuce wurin. Alal hakika ma don warware matsalolin da muka ambata a rubutuna na shekaranjiya ne aka dau lokaci tsakanin 2019 zuwa yanzu.

Tsoronmu na yanda za a kai shi teku, ko a sarrafa shi a nan, ko wani shugaban ya tsaida aikin da na nemo wasu rijiyoyin nan gaba duk an warware su.

Tabbaci

A kan batun tabbacin ci gaba da farautar feturn a kan tudu, da farko dai dokar PIA ta ware 30% na ribar NNPC musamman don haka. Jazaman.

Na biyu kuma, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ba da tabbacin in Allah ya ba shi mulki zai ci gaba da wadannan ayyuka. Tabbaci kuma wanda daga yanda fuskar da ya fadeshi ta nuna, da gaske ya ke yi. Ah. Ko ba komi sai mutanensa sun fi mu morar ayyukan tunda su ke da kudin zuba jari. Don haka ya tsayar da ayyukan ma asara ce, sai dai idan zai yanke hancinsa ne don ya bata wa fuskansa rai, inji Turawa.

Sauran yan takara ma ya kamata mu ji nasu.

Kudi

Na farko dai kamfanin SEEPCO, wanda shi zai yi aikin haka da sarrafawar, kamar yanda shugabansa Mr. Mohit Barot ya ce, ya riga ya tanadi kudi lakadan, watau suna nan a jibge, wanda ake bukata na aikin. Tun da na ji haka na ce, “Af! Aikin gama ya gama.” Sai shukura.

Matatar Mai

SEEPCO zai gina matatar mai a kusa inda za a rika
1) Tace har ganga 120,000 na fetur a wuni daya.
2) Samar da gas 500,000 cubic meters a wuni daya
3) Tashar samar da lantarki ta gas din mai karfin 300MW
4) Takin zamani na 2,500 tonnes (buhu 50,000 a wuni daya.

Shagali

Kaddara an samu nan gaba kadan a fadamun Sokoto, Bida, Benue da Chad. 

Tabdi jam. Gaskiya a gaya wa Baba, mu fa ko Arewa ba mu yi sharholiya ba, za mu yi shagali, in sha Allahu. Sai dai ya yi hakuri. Ehe. 😁

Dr. Aliyu U. Tilde
Bauchi
23 November 2022