On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Aiwatar Da Dokar Kare Hakkin Kananan Yara Zai Cika Burin Gwamnatin Kano Na Kawar Da Almajirai Daga Tituna – Kungiya

Wata kungiya mai rajin kare hakkin al’umma, Bridge Connect Africa Initiative, ta kalubalanci gwamnatin jihar Kano da ta gaggauta tabbatar da kudirin dokar kare kananan yara da kuma aiwatar da shi, amatsayin kudurin da ta dauka na kawar da almajirai daga kan tituna a jihar Kano.

Da yake zantawa da manema labarai a karshen mako, Babban Daraktan kungiyar, Sani Muhammad, ya bayyana cewa jinkirin amincewa da kudirin na jefa yara mata da kananan yara cikin hadarin afkawa irin wannan matsala da fantsama a tituna.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa, idan a karshe gwamnatin jihar Kano ta rattaba hannu kan dokar kare hakkin yara ta 2018, za ta kare da kuma hana yiwa ‘ya’ya mata auren wuri da kuma auren dole.

“Da zarar an zartar da kudurin dokar, ya zama laifi ga kowa ya ci zarafin yara ta hanyar  lalata, domin duk wanda aka kama zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari acewar daraktan.

"Wannan yana nufin cewa za a sami raguwar lalata da yara a cikin jihar," in ji shi.

Kudirin kare hakkin kananan yara na jihar Kano wani kudiri ne mai muhimmanci, idan har aka amince da shi, zai amfanar da dukkan yara a jihar Kano.”

“Idan har aka amince da kudurin, dokar ta tanadi cewa idan mace ta dauki ciki kafin ta kammala karatunta, za a ba ta tallafin karatu da damar yin karatun bayan haihuwa don ci gaba da karatun ta" Inji Sani Muhammad.