On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Akwai Aikin Gyara Kura-kuran Ganduje A Gaban Sabuwar Gwamnatin jIhar Kano - Ibrahim A Waiyya

Shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula a Kano, Ibrahim A Waiya ya ce dole ne sabuwar gwamnati mai dake tafe  ta gyara barnar da gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ta yi.

Waiya ya yi wannan tsokaci ne a kan rokon gafarar da gwamnan ya yi dake  neman gafarar wadanda watakila ya yi musu laifi a lokacin da yake kan mulki.

Ya nemi yafiyar  a lokacin da yake jawabi a wani taron lacca na watan Ramadan a Kano.

Waiya, wanda ya jaddada cewa babu laifi a kan gwamnan ya nemi afuwar jama'a, sai dai ya ce ya rage ga wadanda aka yiwa laifi su amince da rokon.

Ana saran gwamnan zai kammala wa’adinsa na biyu na shekaru takwas a wata mai zuwa tare da mika ragamar shugabancin ga zababben Gwamna, Abba Kabir Yusuf.