On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Akwai Bukatar Hafsoshin Tsaron Najeriya Su Ajiye Mukamansu - Farfesa Usaman Yusuf

Wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum kuma mamba a kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Usman Yusuf ya yi kira ga manyan jami'an sojojin Najeriya su yi murabus daga kan mukamansu  sakamakon harin da jirgin yaki ya kai kan fararen hula a Kaduna  ranar Lahadi.

Yusuf ya ce a wani yanayi na daban, akwai bukatar  dukkan hafsoshim soji su mika takardar murabus dinsu kan hadarin da ya jefa kasarnan cikin alhini.

Ya kuma bayyana cewa rundunar  Sojoji ba za su iya bincikar kanta ba, don haka ya kamata a samu wani kwamiti mai cikakken iko, mai zaman kansa karkashin wani babban Alkalin Alkalan Najeriya mai ritaya, domin ya binciki al'amarin.

Ya ce kasashen waje za su yi shakkar sayar da makamai ga sojojin Najeriya muddin suna Afkawa Fararen hula.