On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Akwai Bukatar Samar Da Kwamitocin Sa Ido Kan Cin Zarafi A Makarantun Jihar Kano - CITAD

Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma CITAD ta ce akwai bukatar a samar da Kwamitocin sanya idanu akan matsalolin cin zarafi a makarantu da ke jihar Kano

Babbar Jami’ar mai kula da harkokin jinsi da kula da shirin yaki da cin zarafi a cibiyar Zainab Aminu itace ta bayyana hakan yayin taron manema labarai na wata-wata.

Tace Cibiyar ta samu rahoton aikata laifuka cin zarafin mata guda 100 a watan da ya gata cikin rahonni 140 da ta samu  a watan Yuli na 2022.

Zainab ta nunar da cewa a tsukun  lokacin, CITAD tana samun rahotannin cin zarfin ne ta hanyar manhajar wayar hannu da ta samar.

Ta yaba da kokarin duk masu ruwa da tsaki ke yi wajen wayar da kan jama'a game da matsalolin cin zarafi, yayin da ta  bukaci jama'a da su ci gaba da bayar da rahoton cin zarafi don samun nasarar tsaftace al'umma daga matsalar.

Zainab Aminu ta yi kira ga Gwamnati da Majalisar Dokoki a Jihar Kano  da duk masu ruwa da tsaki da su tabbatar dokar kare hakkin yara  da kuma sake fasalta kundin hukunta manyan laifuka.

Haka kuma tayi kira a samar da kotu ta musamman domin maida hankali kachokan akan matsalolin cin zarafi  a cikin al'umma.