On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Offishin Jakadanci Ya Bukaci Yan Najeriya Da Suka Makale A Sudan Su Cigaba Da Zama A Gida

Tarayyar Najeriya ta sake jaddada bukatar  daliban Najeriya da ke kasar Sudan su kasance a gida yayin da take ci gaba da shirye-shiryen kwaso su daga kasar mai fama da rikici.

A sanarwar da Ofishin Jakadancin Tarayyar Najeriya a birnin Khartoum, ya fitar a ranar Lahadi ya tabbatar da matakin gwamnatin.

Sanarwar ta shawarci daliban da su yi watsi da sanarwar da kungiyar dalibai ta kasa NANS a Sudan ta fitar, inda ta yi kira ga daliban da su hadu a ofishin NANS kuma su kawo dala 100 ko dala 200 domin kwashe su.

Gwamnatin tarayya  ta ce har yanzu yana da hadari a fara tattaki zuwa kan iyakokin Sudan ba tare da samun tabbacin tsaro daga  hukumomin Sudan ba.

An kashe daruruwan mutane tun bayan da aka fara  gwabza fada tsakanin dakarun janar-janar guda biyu a birnin Khartoum.