On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Alhazan Najeriya Dubu 10 Sun Rasa Tantina A Mina

MINA

Hukumar aikin hajji ta kasa, Ta baiyana rashin bacin ranta akan karancin Tantanina ga wasu Alhazan Najeriya kimanin dubu 10, a Muna, Wanda wani kanfanin kasar Saudiya ke aikin samar da Tantinan ga Alhazan Najeriya.

Shugaban hukumar, Alhaji Zikirullah Kunle ne  ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Muna, Kazalika  ya  ce bai ji dadin  yadda aka tsara ciyar da alhazan a filin Muna ba, kasancewar  abincin bai wadata ba, sannan kuma  ya zo a makare.

Ya kara da  cewar  tun da  farko  sunyi tunanin samun wannan matsala,wanda  hakan  tasa  suka  baiwa  hukumomin saudiyya  shawarar  shigar dasu  cikin tsarin  ciyarwar, amma  suka  tilasta cewar suna da wani  tsarin ciyarwa  na bai  daya.

Shugaban hukumar aikin hajji ta kasa, Ya ce tuni  suka  sanar da ma’aikatar aikin hajji  da umarah ta saudiya  koken da  Alhazan Najeriyar  suka yi,  domin  daukar matakin da ya  da ce.

Sai dai a wani bangaren 