On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Ambaliyar Ruwa Ita Ce Jigon Rahotonmu Na Wannan Makon

Saturday, 24 September 2022 10:34

By Abdulmumin Abubakar Tsanyawa

Tambarin idon Mikiya Na Arewa Radiyo

Gagarumar ambaliyar ruwa da aka fuskanta biyo byan tumbatsar maragar ruwa ta dam din Tiga dake jihar Kano tayi awon gaba da kimanin gonaki dubu sha shida da dari shida da arba’in da hudu a kananan hukumomin Rano da Bebeji da Warawa da Wudil da kuma Dawakin Kudu a jihar Kano.

Hakan dai nada alaka da mamakon ruwan sama da ake ta samu a kwanakin baya a cikin jihar Kano dama makwaftan jihohi da suka hadar da Kaduna da Bauchi da Plateau, wanda kuma yayi sanadiyyar lalata gonaki a kananan hukumomin da abun ya shafa.

Rahoton mu na musamman na wannan mako,  da wakilin mu Victor Christopher ya hada mana ya maida hankali kan makomar manoman da ambaliyar ruwan tayi awon gaba da gonakin su. Ga Kamaludeen Muhd da fassarar rahoton.

Latsa sautin domin sauraren cikakken Rahoton  na  VICTOR  CHIRISTOPHER....