On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Ambaliyar Ruwa Mafi Muni Cikin Shekaru 50 Ta Afkawa Wasu Yankunan Kasar Sin.

An kwashe dubunnan daruruwan mutane a kasar Sin a wasu lardunan kudanci da gabashin kasar bayan da aka samu ruwan sama mai karfin gaske da ya haddasa ambaliya da zabtarewar kasa.

Ambaliyar ta haddasa tumbatsar   koguna sannan  kuma itace mafi muni da aka gani cikin tsawon shekaru 50.

Hotunan bidiyo da kafafen yada labarai na kasar suka fitar sun nuna yadda ake tsamo motoci da suka makale a tituna, da kuma ceto mutanen da igiyar ruwa  ta ja.

An bukaci Mutanen da ke zaune a gefen kogi  da su gaggauta  tashi daga wajen.