On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Amfani Da Karfin Soja Ba Zai Kawo Nasara Ga Yaki Da Matsalolin Tsaron Najeriya Ba - Sanata Yarima

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Yerima, ya bada shawarar cewa ya kamata shugaba Bola Tinubu ya fara tattaunawa da ‘yan bindiga maimakon amfani da karfin soja.

Ya ce matakin shi ne hanya mafi dacewa ta magance kalubalen rashin tsaro don magance tashe-tashen hankula a kasarnan.

Yerima ya bayar da shawarar a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ziyarar ban girma da ya kai wa shugaban a ranar Litinin.

Sanata Yerima ya ce gwamnatin da ta shude ta gaza wajen tattaunawa da ‘yan bindigar, yana mai cewa  tattaunawar za ta samu ci gaba kamar yadda aka samu da tsagerun Neja Delta.