On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Amnesty International Ta Bukaci Tura Rundunar Kare Fararen Hula Zuwa Sudan

Nura Mudi Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Kasa da Kasa Amnesty International ta yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya, Tarayyar Afirka da ƙasashen duniya da su gaggauta tura rundunar kare fararen hula zuwa Sudan, tana mai gargadin cewa yaƙin da ya shafe shekaru uku ana yi a ƙasar ya rikide zuwa ɗaya daga cikin mafi munin bala'o'in jin ƙai a duniya.

Ƙungiyar ta ce tun bayan ɓarkewar rikicin a shekarar 2023, dubban mutane sun rasa rayukansu, yayin da kusan mutum miliyan 14 suka rasa matsugunansu sakamakon kashe-kashe da cin zarafi, fyade da fashi da lalata dukiyoyi.

An bayyana hakan ne a Kano yayin gabatar da sabon rahoton Amnesty International mai taken "City Under Siege, Children Under Fire", wanda ke bayyana irin ta'asar da ake zargin dakarun Rapid Support Forces (RSF) suka aikata a birnin El Fasher da ke Jihar Arewacin Darfur.

Da yake jawabi, Daraktan Amnesty International Najeriya, Isa Sanusi, wanda ya wakilci Shugaban Kwamitin Amintattu na ƙungiyar, Auwal Musa Rafsanjani, ya ce rahoton da aka ƙaddamar a ranar 1 ga watan Yulin 2026 ya ƙunshi hujjoji masu ƙarfi da ke nuna cewa RSF sun aikata laifukan cin zarafin bil'adama.

Ya ce, "Rikicin Sudan ya  zama Iftila'in jin ƙai da ke ci gaba da hallaka dubban fararen hula tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu."

Sanusi ya bayyana cewa Sudan na da muhimmanci ga Najeriya da nahiyar Afirka baki ɗaya saboda tsohuwar alaƙar tarihi, kasuwanci, ilimi da addini tsakanin ƙasashen biyu.

A cewarsa, Sudan ƙasa ce mai yawan jama'a kusan miliyan 51, wadda ke da jami'o'i 56 da suka kasance cibiyoyin ilimi ga dubban ɗalibai daga ƙasashe daban-daban, ciki har da Najeriya.

Ya ƙara da cewa akwai tsakanin mutum miliyan uku zuwa bakwai 'yan Najeriya da ke zaune a Sudan, musamman daga ƙabilun Hausa, Fulani da Kanuri.

Sanusi ya bayyana cewa tun bayan tsanantar rikicin, an kwaso aƙalla 'yan Najeriya 3,100 daga Sudan, mafi yawansu ɗalibai ne da yaƙin ya katse musu karatu.

Ya jaddada cewa, "ba za a iya ci gaba da kallon abin da ke faruwa a Sudan ba tare da ɗaukar matakin gaggawa ba. Lokaci ya yi da duniya za ta kare rayukan fararen hula."

"Duk wanda ya aikata laifukan yaƙi ko cin zarafin bil'adama, ba tare da la'akari da matsayinsa ba, dole ne ya fuskanci hukunci."

Da yake gabatar da cikakken binciken rahoton, mai bincike kan Sudan na Kungiyar Amnesty International, Abdullahi Hassan, ya ce binciken ya gano yadda dakarun RSF suka kai hare-hare kan ƙauyuka 22 da ke kewaye da El Fasher, inda suka aikata kashe-kashe ba bisa ƙa'ida ba da fyade, sace dukiyoyi da lalata gidaje da muhimman kayayyakin more rayuwa na al'umma.

"Bincikensu ya nuna cewa abin da ya faru a El Fasher ba kawai rikici ba ne, laifukan cin zarafin bil'adama ne da suka haɗa da kashe-kashe, fyade, sace dukiyoyi da lalata ƙauyuka."

Abdullahi Hassan yace yara ne suka fi shan wahalar rikicin, inda da dama suka rasa rayukansu, yayin da daruruwa suka zama 'yan gudun hijira a cikin ƙasarsu.

"Yara da dama sun rasa rayukansu, wasu kuma sun zama 'yan gudun hijira a cikin ƙasarsu abun takaici."

Ya kuma yi gargadin cewa ci gaba da bai wa ɓangarorin da ke yaƙi makamai na ƙara ta'azzara rikicin.

"Ba za a kawo ƙarshen wannan bala'i ba muddin ana ci gaba da samar wa ɓangarorin da ke yaƙi makamai."

Amnesty International ta buƙaci a tsagaita wuta cikin gaggawa a faɗin Sudan, kuma a tura rundunar kare fararen hula tare da amincewar Majalisar Ɗinkin Duniya, a faɗaɗa takunkumin hana kai makamai zuwa Darfur, da kuma dakatar da duk wata ƙasa ko ƙungiya da ke ci gaba da bai wa ɓangarorin rikicin makamai.

Ƙungiyar ta kuma yi kira da a ƙarfafa kariya ga yara da sauran fararen hula, tare da tabbatar da adalci da hukunta duk masu hannu a aikata laifukan yaƙi da cin zarafin bil'adama.

A cewar ƙungiyar, "Adalci shi ne ginshiƙin zaman lafiya. Ba za a samu zaman lafiya mai ɗorewa ba idan ba a hukunta masu aikata waɗannan laifuka ba."

Amnesty International ta kuma buƙaci ƙasashen duniya su ƙara tallafawa bincike da gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata waɗannan munanan laifuka domin tabbatar da cewa babu wanda zai tsere wa hukunci.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 33°C | Low: 23°C