On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Amurika Ta Gargadi 'Yan Kasarta Su Guji Zuwa Wasu Wurare A Najeriya

Ofishin Jakadancin Amurika

ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ya gargadi Amurikawan dake cikin kasar nan da su guji yin balaguro zuwa wasu wurare a Abuja da kuma wasu jihohi 19 na kasar nan.

Jihohin sun hada da Borno da Yobe sai Adamawa da Gombe da Kaduna sai jihar  Katsina da  Zamfara da wasu yankuna na jihar Delta sai  Bayelsa da  Rivers da Akwa Ibom da kuma jihar Cross River.

An kuma shawarce su da  su guji yin wata  tafiya matukar ba mai muhimmanci bace zuwa jihohin  Bauchi da Kano sai Jigawa da Niger  da  Sokoto da Kogi da  Kebbi sai Abia da Bayelsa sai  Rivers da Plateau  da kuma jihar  Taraba.

Wannan mataki na  zuwa ne sa’o’i 24   bayan da  ‘yan ta’adda suka kai hari gidan gyaran hali na kuje dake Abuja.