Rundunar sojin Amurka ta ce zirga-zirgar jiragen ruwa na cigaba da gudana a mashigar ruwan Hormuz, duk da ikirarin da Iran ta yi na cewa ta rufe mashigar sakamakon sabon rikicin da ya sake barkewa a Gabas ta Tsakiya.
Rundunar CENTCOM, wadda ke kula da ayyukan sojin Amurka a yankin, ta bayyana a shafinta na X cewa Iran ba ta da ikon rufe mashigin, tana mai jaddada cewa hanyar ruwan na ci gaba da kasancewa a bude ga zirga-zirgar jiragen ruwa. A wata sanarwa ta gaba, CENTCOM ta kalubalanci ikirarin Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC), tana mai cewa mashigin Hormuz hanya ce ta kasa da kasa, kuma dakarun Amurka na shirye su tabbatar da ci gaba da bude ta. A lokaci guda da Iran ta sanar da rufe mashigin, ta kuma kai hare-hare kan wasu kasashen yankin Gulf da ke kawance da Amurka, lamarin da ya kara jefa yarjejeniyar tsagaita wuta cikin hadari yayin da ake ci gaba da kokarin cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta dindindin.
Comments
Add a comment