On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Amince Da Dokar Daidaita Kudin Aure A Jihar Sokoto

DAURIN AURE

A ranar Talata ne Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta amince da kudirin dokar daidaita kudin aure a jihar.

Kudurin dokar wadda Alhaji Abubakar Shehu   na jam’iyyar  APC dake wakiltar Yabo da Faruk Balle  na jam’iyyar  PDP  dake  wakiltar  Gudu suka gabatar, an fara  mika shi gaban  kwamitin kula da harkokin addini na majalisar domin yin nazari a kansa.

Alhaji Abubakar Shehu   wanda shi ne shugaban kwamitin, ya gabatar da rahoton a zauren majalisar a  jiya, inda  majalisar  ta amince dashi.

Kudirin dokar dai ya tanadi kula da yadda ake kashe makudan kudade wajen auratayya  ko  bukin  suna da sauran bukukuwa  na al’ada  da ake yi a jihar.