On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Bada Umarnin Rufe Ofishin Jakadancin Najeriya A Mexico Saboda Corona

Za a rufe ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar Mexico na tsawon kwanaki bakwai sakamakon bullar cutar COVID-19 da ta kama wasu ma’aikatan ofishin guda shida.

Jakadan Najeriya a Mexico Adejare Bello shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Jakadan ya tabbatar da cewa a halin yanzu ma’aikatan da abin ya shafa suna samun kulawa sosai, ya kara da cewa suna hannun jami’an lafiya da suka dace wadanda suka tabbatar masa da cewa ana.shawo kan lamarin.

 A cewar sanarwar an sanar da bangarorin da suka dace kamar ma'aikatar harkokin wajen Najeriya  a Abuja da na Mexico halin da ake ciki.