On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

An Binne Mutane 71 Daga Cikin 84 Da 'Yan Bindiga Suka Halaka A Katsina

'Yan Ta'adda

Rahotannin da ake samu na tabbatar da cewar, yawan wadanda ‘yan ta’adda suka haka a jihar Katsina, ya karu zuwa Tamanin da hudu.

Yan  ta’addar sun yiwa tawagar   ‘yan  sa kai  kwantan bauna a  dajin  Yar goje  dake cikin karamar hukumar  Kankara a  cikin ta katsina a ranar  Lahadi, a  lokacin da suka  durfafi  cikin  dajin, da zummar kwato  shanun da aka sace  daga  yankin.

Mazauna  garin sun tabbatar da  cewa  sun binne  gawarwarki sama da guda  saba’in a  halin yanzu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi All..h  wadai  da harin  na  ‘yan ta’adda  wanda  ya  baiyana  a matsayin  na tashin hankali.

A  sanarwar  da  shugaban kasar  ya fitar  ta hannun Kakakinsa,Malam  Garba  Shehu,Ya  ce , ba  za’a  manta da irin  sadaukarwar  da jami’an sa kan  suka  yi ba.