On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Bukaci A Sulhunta 'Ya'yan Jam'iyyar APC Da Aka Batawa Rai A Kano.

ABDULLAHI ABBAS SHUGABAN JAM'IYYAR APC A KANO

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC reshen jihar Kano, Sun bukaci Manyan jam’iyyar dasu samar da wani tsari na yin sulhu, domin kwantar da jijiyar wuyan ‘yayan jam’iyyar da aka batawa rai, gabanin babban zaben kasar nan na shekarar 2023 dake tafe.

Masu ruwa da tsakin sun yi wannan roko ne , a yayin da  shugabannin jam’iyyar na shiyyar Arewa maso yamma  a karkashin jagorancin mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin, Salihu Lukman suka yi wata ganawa dasu, a cigaba da rangadin da suke yi.

Wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na shiyyar Arewa maso yamma, Malam Musa Mailafiya Mada ya fitar, yace  yadda  za’a kan jam’iyyar wuri daya shine abunda akafi maida hankali a yayin ganawar.

Sanarwar ta kuma baiyana cewa gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu wakilcin shugaban Ma’aikatansa wanda kuma shine shugaban ma’aikata na jihar Kano, Ya baiyana gamsuwarsa  da irin yadda ake tafiyar da harkokin jam’iyyar APC a yankin Arewa maso yammacin kasar nan.