On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

An Bukaci Bincike Kan Zargin Mutuwar Wani Mutum a Hannun EFCC

Jami'an Hukumar EFCC

An samu tashin hankali a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano bayan rasuwar wani mutum da iyalansa ke zargin ya mutu ne yayin da yake tsare a hannun Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati (EFCC), sakamakon wata takaddama kan mallakar fili.

Rahotanni sun bayyana cewa an tsare Alhaji Yahaya Musa ne bisa wani zargi da ke da alaƙa da rikicin mallakar wani fili tsakaninsa da wani mutum mai suna Murtala.

Iyalansa sun buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya haddasa mutuwarsa.

Da take zantawa da wakilinmu, Ado Danladi Farin Gida, matar mamacin, Hajiya Hadiza Yahaya, ta yi zargin cewa mijinta ya rasu ne yayin da yake tsare a hannun EFCC bayan an kai ƙarar rikicin filin ofishin hukumar da ke Kano.

Ta buƙaci a gudanar da sahihin bincike cikin gaskiya da adalci domin tabbatar da musabbabin mutuwar.

Bayan taƙaddamar da ta ɓarke a asibitin, Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta shiga tsakani ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda, A. S. Gusau, wanda ya roƙi iyalan mamacin su karɓi gawar domin yi mata jana'iza, tare da ba su tabbacin cewa rundunar za ta gudanar da cikakken bincike tare da tantance duk wata hujja da za su gabatar domin gano gaskiyar abin da ya faru.

Wata majiya daga shiyyar Kano ta Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati (EFCC), wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta musanta zargin da ke alaƙanta mutuwar marigayi Alhaji Yahaya Musa da tsare shi a hannun hukumar.

Majiyar ta ce marigayin ya sanar da jami'an EFCC cewa yana fama da cutar hawan jini, har ma ya nuna musu magungunan da yake sha, lamarin da likitocin hukumar suka tabbatar.

A cewar majiyar, marigayin ya daina halartar kotu tun bayan da aka ba shi beli a watan Nuwamban shekarar 2025, kafin daga bisani jami'an EFCC su sake kama shi a harabar Kotun Nomansland da ke Kano, inda ya je domin wata shari'a ta daban.

Majiyar ta ƙara da cewa jim kaɗan bayan an gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke kan titin Court Road a ranar Litinin, marigayin ya faɗi ƙasa bayan alƙalin kotun ya ɗage zaman na ɗan lokaci. Nan take aka garzaya da shi zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa. Ta kuma ce EFCC na duba hotunan kyamarorin tsaro (CCTV) na harabar kotun kafin fitar da sanarwa a hukumance kan lamarin.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 35°C | Low: 24°C