On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Bukaci Jama'a Su Koma Hawan Keke Tunda An Cire Tallafin Mai

LAULAWA

Gabanin bikin ranar hawa Keke ta duniya da ake yi duk ranar 3 ga watan Yunin kowacce shekara, kungiyar masu hawa kekuna ta duniya, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi amfani da kudaden tallafin mai wajen inganta harkar sufurin hawan keke wanda hakan zai temaka wajen dakile matsalar sufuri da tallafin cire tallafin man ya haifar.

Da yake ganawa da  wakilinmu, Mataimakin Shugaban kungiyar , John Emmanuel ya bayyana cewar samar da ingantaccen tsarin sufuri,  shi  ne mafita  ga  jama’a a halin yanzu.

Ya kuma ce  sakamakon cire  Tallafin mai da aka yi , A halin yanzu  hawan keke shi  mafi  rahusa ta  bangaren  sufuri, wanda  yafi  dacewa da  yin  zirga-zirga   ta kimanin   nisan kilomita 10  zuwa  15.

Ya bayyana cewa ana kan aiwatar da wani sabon tsarin inganta  sufurin hawa  kekuna na kasa, sannan ya bukaci Gwamnati da ta janye duk  wani nau’in  haraji da aka saka  kan shigo da Keke  a kasar  nan.