On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Cafke Daya Daga Cikin Fursunonin Da Suka Arce Daga Gidan Gyaran Hali Na Kuje A jihar Katsina

kuje attack

Jami’an yansanda sun dakume wani mai suna Kamal Lawal Abubakar Mazaunin unguwar Sale dake cikin karamar Hukumar ‘Dan musa ta jihar Katsina.

Abubakar  wanda ake zargin yana daya daga cikin wadanda suka cika wandonsu da iska daga gidan gyaran hali na Kuje dake Abuja, An kamashi ne da yammacin jiya, a sakamakon wasu bayanan sirri da  baturen yansandan yankin da kuma jami’ansa suka samu, wanda hakan yasa suka  kaddamar da sumame akan maboyar masu aikata lefuka dake cikin karamar hukumar.

A lokacin da ake caka da bincike, wanda ake zargin ya tabbatar da cewa  yana daga cikin wadanda suka arce daga gidan gyaran hali na Kuje dake Abuja, alokacin harin kwanan nan da aka kai.

Mai magana da yawun rundunar yansandan jihar Katsina, SP Gambo Isah  yace  an samu busasshen ganyen tabar wiwi a wajen kamal Lawal a lokacin da jami’an yansanda ke bincike, sannan kuma ya tabbatar da cewa  za’a mika shi hannun hukumar kula da gidajen gyaran hali ta kasa domin daukar mataki na gaba.