On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An 'Dage Lokacin Yanke Hukuncin Shari'ar Tsohon Gwamnan Filato Jonah Jang.

Tsohon Gwamnan jihar Filato Jonah Jang

Babbar kotun jihar Filato ta dage lokacin da zata yanke hukunci akan shari’ar da ake yiwa tsohon gwamnan jihar, Sanata Jonah David Jang, Da kuma tsohon mai kula da harkokin biyan kudi na Ofishin Sakataren gwamnatin jihar Yusuf Pam.

Tsohon gwamnan jihar Jonah Jang da kuma Yusuf Pam na fuskantar shari’ar ne bisa zarginsu da aikata lefin cin amana tare da yin wadaka da wasu kudaden jihar har naira bilyan 6 da milyan 300.

A yayin cigaba da zaman shari’a na jiya, Lauyoyin wadanda ake kara sun amince da cewar sun kammala gabatarwa da kotu abunda suke dashi, inda suka bukace ta  data  sallame su  sannan kuma ta wanke su daga dukkanin zarge-zaregen da ake yi masu.

Lauya mai gabatar da kara, Rotimi Jacob SAN, Ya bukaci tayi la’akari da dukkanin shaidu 14 da aka gabatar mata, musamman shaida  ta biyar da aka gabatar a shari’ar wanda  ta tabbatar da aikata abunda ake zargin mutum na biyu a cikin shari’ar da aikatawa.