On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Dakatar Da Ayu Daga Shugabancin Jam'iyyar PDP

Jam’iyyar PDP ta sanar da dakatar da shugabanta na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, bisa zargin  yiwa jam’iyyar zagon kasa.

Shugabannin zartaswa na  PDP a mazabar Igyorov da ke karamar hukumar Gboko a jihar Benue sune suka  dakatar da Ayu.

Sakataren mazabar na  PDP, Vangeryina Dooyum, ya ce an cimma wannan matakin ne bayan da shugabanni sukayi nazari kan babban zaben da aka kammala.

Idan za’a iya tunawa  jam’iyyar PDP a matakin jihar ta Benuwe a karshen mako ta kada kuri’ar amincewa da Gwamna Samuel Ortom, wanda shugabancin zartarwa na kasa ya mikawa kwamitin ladabtarwa domin bincike kan shugaban jam’iyyar.

Anyi zargin cewa matakin ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke na hana PDP daukar duk wani mataki na ladabtarwa akan Ortom har zuwa lokacin da za a yanke hukunci.