On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Dakatar Da Cigaba Da Karbar Kudin Ajiya Daga Maniyata Aikin Hajjin 2023 A Jihar Kano

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Kano ta sanar da rufe cigaba da karbar kudin ajiya daga maniyyatan da ke shirin gudanar da aikin Hajjin 2023

Idan za a iya tunawa,  hukumar ta sanya Naira milliyan 2 zuwa milliyan 2 da Rabi  ga maniyyatan da ke da niyyar sauke farali  a bana biyo bayan matakin gwamnatin  Saudiyya na dawowa da Najeriya guraben  kujeru dubu  95  tare da cire duk wasu ka’idojin COVID-19.

Da yake yiwa manema labarai jawabi a ranar Alhamis a Kano, Sakataren zartarwa na hukumar Jin dadin alhazai ta  jihar Kano,  Muhammad Abba Dambatta, ya ce daga yau hukumar ta rufe karbar duk wani sabon kudin  ajiya daga maniyyata zuwa lokacin da za'a kammala aikin tantance wadanda suka riga suka  biya naira miliyan biyu ko milliyan 2  da rabi. 

Ya kuma musanta wata jita-jita game da ainihin adadin kudin kujerar  aikin Hajjin bana.

An shirya fara jigilar maniyan Najeriya zuwa  Hajjin 2023 a cikin watan Mayu nan da kwanaki 30 masu zuwa.