On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Dakatar Da Wasu Shugabannin Kananan Hukumomi Ukku A Jihar Jigawa

JIGAWA

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da wasu shugabannin Kananan hukumomi guda Ukku, saboda zarginsu da yin balaguro zuwa kasashen ketare batare da samun wani izini daga bangaren zartarwa ko kuma majalisar dokokin jihar ba.

Shugabannin da aka dakatar sun hada da Shugaban karamar hukumar Birniwa  Mubarak Ahmed   sai Rufa’i Sunusi na karamar hukumar Gumel  da  kuma Umar  Baffa wanda ke  zama  shugaban karamar hukumar Yankwashi, inda aka ce  sunje kasar Rwanda  batare da samun izini ba.

Daukar matakin da majalisar dokokin jihar ta Jigawa  ta yi, ya biyo  bayan  kudirin da shugaban kwamitin kula da kananan hukumomi a zauren majalsiar, Aminu Zakari Tsubut  ya  gabatar akan shugabannin kananan hukumomin da abun ya shafa.

Ya  ce   zauren majalisar  ya umarci   shugabannin kananan hukumomin da  kada su yi  wata  tafiya  zuwa wani  kafin  gabatar da kudirin kasafin kudin sabuwar shekara, amma suka bijirewa umarnin.

Ya kuma baiyana halaiyar  da suka nuna a matsayin rashin ‘Da’a  da  kuma nuna sakaci wajen sauke  nauyin dake kan wuyan su.