On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

An Da'kume Wasu Ri'Ka'K'Kun Masu 'Kwacen Waya A Kano.

SP ABDULLAHI Haruna kiyawa

Rundunar ‘yansandan jihar kano ta tabbatar da Cafke wasu Rikakkun masu yin kwacen waya da suka addabi Fasinjoji da kuma al’ummar kan titin stae Road da titin zariya, ta hanyar amfani da baburan adai-daita sahu mai dauke da Lambar KAROTA, KBY 0126

 Wadanda  ake  zargin  na ‘badda  kama  a matsayin  matuka  baburan  adai-daita sahu  sun  hadar  da  Muhammad  Jidda  mai shekaru 20  sai  Adamu  sulaiman  mai  shekara 22  a Duniya  Dukkanninsu  mazauna   unguwar  Birgade

 Hakan  dai  na  kunshe  ne cikin  wata   sanarwa  mai  dauke  da sa  hannun  kakakin  Rundunar yansandan jihar Kano, SP Haruna  kiyawa da aka fitar,  wanda  yace  kamen  ya  biyo  bayan  korafe-korafe  babu  kakkautawa  daga  al’ummar  yankunan  akan  ayyukansu  na  yin  kwace  waya