On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

An Fara Rigakafin Cutar Anthrax A Abuja

ANTHARAX

Hukumar birnin taraiyya A buja ta fara aikin rigakafi ga mutane sama da milyan daya dake birnin taraiyya Abuja, domin dakile barkewar cutar Anthrax.

Mukaddashin sakataren hukumar birnin taraiyya Abuja, Alhaji Ishaq Sadeeq  shine  ya  jagoranci  kaddamar da rigakafin wadda  za’a dauki tsawon makwanni hudu ana gudanar da ita  a  karamar  hukumar Gwagwalada  dake  Abuja.

Ya ce  daukar matakan rigafin ya zama wajibi  sakamakon samun bullar cutar a jihar Naija, wadda  ta kasance  makociyar  Abuja.