On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

An Fara Saka Kyamarorin Tsaro A Jiragen Kasa

JIRAGEN KASA

Biyo bayan sauyin lokacin da za’a dawo zirga-zirgar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna, A yanzu haka gwamnatin taraiya ta fara saka kyamarorin tsaro a dukkanin taragun dake cikin jiragen kasar.

Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan da ministan sufuri, Mu’azu Sambo  ya bada sanarwar  dage lokacin da za’a dawo da zirga-zirgar jiragen kasar.

A jiya ne  ‘yan kwangilar da aka baiwa aikin, suka  fara saka kyamarorin tsaron a tashar jirgin kasa ta Idu dake Abuja.

Kakakin Hukumar Kula da Sufurin jiragen kasa ta Najeriya Mahmood Yakubu, Yaki cewa tak kan matakin lokacin da ake nemi jin ta bakinsa.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 38°C | Low: 24°C