On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

An Fara Samun Dogayen Layin Ababen Hawa A Gidajen Mai Sakamakon Sanar Da Janye Tallafin Mai

‘Yan sa’oi bayan sanarwar da sabon shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya yi na cewar biyan tallafin mai ya zama tarihi a kasar nan, a yanzu haka an fara samun dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai dake Abuja da Legas da kuma wasu jihohin kasar nan.

Rahotanni sun baiyana cewar, Masu ababen hawa  sun cika gidajen mai a  Abuja da Nasarawa da jihar Naija da  tsakar  ranar  jiya,tun bayan  bullar  sanarwar da sabon shugaban kasar  ya fitar.

Kazalika  alamu sunyi nuni da cewar, tun bayan kalaman sabon shugaban kasar, Masu ababen hawa suka   fara  rububin neman man fetir a  gidajen mai dake Abuja da kuma makotanta.

Mafi akasarinsu sun cika  tankin ababen hawansu, saboda  fargabar  janye tallafin man, wanda ake tsammanin litar man fetir  zata haura naira  500.

To sai dai, Kungiyar Dillalan mai  ta kasa mai zaman kanta IPMAN,  ta soki matakin da sabon shugaban kasa  Bola Tinubu ya dauka na janye  tallafin daga sabon watan Yuni da zamu shiga,  kasancewar babu  tanadin hakan a cikin kasafin kudi.

A martanin da  kungiyar  ta yi tab akin kakakinta, Ukadike Chinedu,  ta  ce  kamata yayi sabuwar gwamnatin ta tattauna  da  ‘yan kasuwar mai  kafin daukar irin wannan mataki.

Ya  ce  bai kamata a janye tallafin mai  a kasar nan batare da  gyara matatun man da ake dasu ba,  To sai dai kuma  kungiyar  manyan dillalan mai  ta kasa  MOMAN, Ta soki lamirin inda  ta ce  ya kamata a janye  tallafin man  dungurun- gum.

Babban sakataren kungiyar,Clemen Isong, Ya  ce  Najeriya  na asarar kudin shigar da take samu  ta hanyar  biyan makudan kudi  da sunan biyan tallafin mai.