On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Fara Samun Takaddama Tsakanin Wike da Gwamnonin Jam'iyyar APC

An fara samun zaman doya da man ja tsakanin Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike da kuma Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya dangane da tabbatar da nasarar shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 dake tafe.

Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, Nyesom Wike, ya fayyace cewa goyon bayan da yake bai wa Shugaba Bola Tinubu domin sake zaɓensa a shekarar 2027, ba yana nufin jam’iyyar adawa ta PDP ba za ta tsayar da ’yan takara a sauran zaɓuka ba.

Wike ya ce matsayinsa bai sauya ba na cewa zai tattara tare da jan hankalin mutane domin su goyi bayan sake zaɓen Tinubu, amma PDP na da ’yancin tsayar da ’yan takara a zaɓukan gwamna, Majalisar Ƙasa da Majalisar Dokokin Jiha.

Ministan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Hulɗa da Jama’a da Kafofin Sadarwa na Zamani, Lere Olayinka, ya fitar ranar Talata, inda ya kuma musanta cewa ƙungiyar siyasar hadakar jam’iyyu ta Rainbow Coalition da Wike ya kafa ba ta kulla wata yarjejeniya ce da jam’iyyar APC ba.

Wike ya ce Rainbow Coalition wani dandali ne da mambobin jam’iyyun siyasa daban-daban za su iya amfani da shi wajen tattara goyon baya ga Tinubu.

Sai dai a wani martani, Shugaban Kungiyar Gwamnnin Jam’iyyar APC, kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ce gwamnonin APC ba za su goyi bayan wani abu da ka iya kawo cikas ga sake zaɓen Tinubu ko raunana jam’iyyar mai mulki ba.

Uzodimma ya ƙara da cewa jajircewar gwamnonin APC wajen yakin neman zaɓe ta tsaya ne kan ’yan takarar jam’iyyar a dukkan matakai.

A gefe guda kuma, wannan cece-kuce ta yiwa ɓangaren Kwamitin Rikon Kwarya na PDP da Tanimu Turaki, SAN, ke jagoranta dadi, inda ya yi wa Tinubu da gwamnonin APC ba’a kan rikicin, yana mai cewa Shugaban Ƙasa da jam’iyyar APC za su gamu da matsalar da suka ƙirƙira da kansu.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 34°C | Low: 23°C