On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

An farawa Bawa Sabbin Dakarun Hisbah 500 Horo Na Musamman

DAKARUN HISBAH

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta fara horas da sabbin dakarunta da aka dauka aiki a kwanan nan a fadin kananan hukumomin jihar Kano 44, domin ganin sun gudanar da aikinsu yadda ya dace.

Kwamandan Hukumar Dr Harun Muhammad Sani Ibn Sina, shine ya tabbatar da haka yayin da yake kaddamar da bada horon ga sabbin Dakarun Hisba 500 da aka dauka aiki, a sansanin Horas da masu hidimtawa kasa dake Karaye.

Dr  Harun  Yace  Hukumar tana daukar  bada horo ga dakarunta da muhimmancin gaske  domin ganin ta samun dimbin nasarori , inda yayi kira a garesu dasu yi amfani da horon da suka samu yadda ya kamata.

Sanarwar da Kakakin hukumar Hisba Lawan Ibrahim Fagge ya  fitar, Yace  bada horon ya kunshi Lakcoci da  yin muhawara da kuma motsa jiki wanda zai dauki tsawon kwanaki 7 a nayinsa.