On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Gaza Samun Tabbaci Daga Daular Larabawa Bayan Ikirarin Gwamnati Na Janye Dakatar Da Visa Ga ‘Yan Najeriya

Alamu sun bayyana cewa har yanzu  Hadaddiyar Daular Larabawa ba ta ce komai ba game da dage haramcin biza da aka kakabawa matafiya daga Najeriya a cikin sanarwa a hukumance  bayan shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Mohamed bin Zayed Al Nahyan ya gana da shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya sanar da cewa ganawar da Tinubu ya yi da mahukuntan Hadaddiyar Daular Larabawa, ta warware takaddamar da ke tattare da hana ‘yan Najeriya biza watanni 10 da suka gabata da kuma dakatar da zirga-zirgar jiragen Etihad da Emirates.

Ngelale ya kara da cewa, bisa wannan yarjejeniya mai cike da tarihi, kamfanonin jiragen saman Etihad da na Emirates za su gaggauta dawo da jadawalinsu na  tashi da saukar jiragen sama, ba tare da wani bata lokaci ba.

Sai dai sanarwa mai sakin layi goma da mahukuntan Hadaddiyar Daular Larabawa suka fitar jim kadan bayan kammala taron kuma kamfanin dillancin labaru na Emirates, ya rawaito, babu  wani sharhi  game da dage haramcin bizar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito Kamfanin Dillancin Labarai na Hadaddiyar Daular Larabawa na cewa, Al Nahyan ya bayyana fatansa ne kawai cewa shugabannin biyu za su yi aiki tare domin karfafa alaka tsakanin Daular larabawa  da Najeriya domin amfanin kasashen biyu.