On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

An Gurfanar Da Mutumin Da 'Yan Sanda Suka Kama Da Katinan Zabe A Jihar Kano

Wata Kotun Majistare da ke Kano a ranar Litinin ta bayar da umarnin tsare wani mutum da ake zargi  dauke da  katin zabe na dindindin guda  29 a Kano.

An tuhumi wanda ake zargin, Tasi’u Abdu da  mallakar katinan zabe namutane daban-daban.

Tun da farko, lauyar masu shigar da karadaga  hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Badiyya Lawan, ta shaidawa kotu cewa wanda  ake kara ya aikata laifin ne a ranar 18 ga watan Janairu.

Tayi zargin cewa an kama wanda ake kara ne da katinan zabe guda 29 na mutane daban-daban ba tare da bayar da gamsasshen bayani kan yadda ya samu katunan ba.

Wanda ake kara, ya ki amsa laifinsa.

Daga nan Babban alkalin kotun, Mustapha Sa’ad-Datti ya dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 30 ga watan Janairu, domin yanke hukunci kan neman belinsa.