On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Han Zubar Da Ciki A Kasar Amurika

An fara rufe cibiyoyin kiwon lafiya Na sha Ka Tafi a wasu jihohin Amurka bayan hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke a ranar Juma'a na soke 'yancin da kundin tsarin mulkin kasar ya baiwa matan Amurka na zubar da ciki.

Kimanin rabin jihohin ne ake sa ran za su gabatar da sabbin takunkumi akan matakin bayan kotu ta soke hukuncin da ta yanke na shekaru 50 na Roe v Wade wanda ya halasta zubar da ciki,  A yanzu haka Jihohi 13 sun haramta zubar da ciki nan take tun bayan  sanar da hukuncin.

Sai dai kuma, Shugaban kasar Amurika  Joe Biden ya bayyana hukuncin a matsayin  wani abu mai rudani da tayar da hankali.

A yanzu haka an fara  zanga-zanga a wasu biranen Amurka domin nuna adawa da hukuncin.