On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Jefe Wani Direba Har Lahira A Jihar Ondo

AKURE

Wadansu mutane da suka harzuka Sun jefe wani mutum dan shekara 35 a duniya har lahira,bayan da suka zarge shi da halaka wasu mutane biyu tare kuma da jikkata wasu guda shida a Akure babban birnin jihar Ondo.

Rahotanni sun baiyana cewar mutanen sun harzuka ne bayan da suka zargi mutumin da yin tukin ganganci wanda hakan  yayi sanadiyar  afkawa  wasu Babura  ‘yan Acaba  guda biyar  dake dauke da fasinjoji a wurare daban daban.

Mutanen sun jefe mutumin har lahira  sannan kumasuka  bankawa  motarsa wuta.

Shaidun gani da ido sun baiyana cewa mutane ukku ne suka mutu a nan take, a yayin da wasu da dama suka samu raunika,kamar  yadda  shima kakakin rundunar  yansandan  jihar SP Olufunmilayo Odunlami Omisanya ta tabbatar da  faruwar abun alhinin.

Sai dai kuma ta baiyana cewar ba dan jami’an yansanda  sunyi gaggawar  kai dauki wajen da abun ya faru, Da mutanen da suka harzuka sai sun halaka  hadda iyayen  direban motar.