On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Jibge Jami'an Tsaro Yayin Da Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Zaben Shugaban Kasa

ALKALAI

An jibge jami’an tsaro daga bangarori daban daban a Abuja babban birnin taraiyya a jiya, Gabanin hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa, zata yanke yau, akan masu kalubalantar nasarar da shugaban kasa Bola Tinubu ya samu a zaben da ya gabata.

An baza jami’an Yan sanda masu kwantar da tarzoma da  Jami’an hukumar tsaro  ta CIVIL DEFENCE da sauran jami’an hukumomin  tsaro a  harabar kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa da sauran  wasu muhimman wurare dake  Abujar.

Da safiyar yaune  za’a yanke hukuncin karkashin mai shari’a Haruna Tsammani  da tallafin  Alkalan kotun, Stephen Adah da Monsurat  Bolaji da  Mai shari’a Moses Ugo da kuma Alkali Abba  Mohammed.

Hakan dai na zuwa ne a yayin da dubban magoya bayan  ‘yan   takarar shugaban kasa a zaben da  ya  gabata,  Atiku Abubakar  na PDP da  Peter Obi na jam’iyyar Labour, Da na Bola  Tinubu na jam’iyyar  APC ke dakon ganin yadda hukuncin  zai kaya da  safiyar  wannan rana.