On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Kaddamar Da Kwamitin Bikin Cikar Najeriya Shekara 63 Da Samun 'Yancin Kai

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin mutane 15  domin shirya bikin cikar Najeriya shekaru 63 da samun ‘yancin kai.

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, wanda ya kaddamar da kwamitin a ranar Alhamis a Abuja, ya kuma kaddamar da ayyukan da aka tsara za'a  gudanar domin bikin cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai.

Akume wanda shi ne shugaban kwamitin ya ce za a gudanar da Abubuwan  da aka tsara don gudanar da bikin ne da kwamitin zai kammala.

Ya ce an kafa shi ne don tsarawa da aiwatar da duk wasu ayyukan da aka amince da su da suka dace da bikin cikar Nijeriya shekaru 63 da samun ‘yancin kai a ranar 1 ga Oktoba, na 2023.