On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

An Kai Hari Offishin INEC A Jahar Ebonyi Ta Kudu Maso Gabashin Najeriya

An kone ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC dake garin Iboko a karamar hukumar Izzi ta jihar Ebonyi.

A cewar kwamishinan hukumar ta INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, al’amarin ya faru ne da safiyar ranar  Lahadi.

Yace, shugabar hukumar  a jihar Ebonyi, Mrs Onyeka Pauline Ugochi, ta rawaito cewa al’amarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safe lokacin da wasu da ba a san ko su waye ba suka kona ginin gaba daya.

A cewarsa, duk da cewa ba a samu asarar rai ba, sakamakon harin, amma ginin da kuma duk wani abu dake cikinsa ya lalace.

Ya koka da cewa wannan shi ne hari na uku da aka kai ofishin karamar hukumar ta INEC cikin kasa da makwanni uku bayan hari makamancin haka a ofisoshin hukumar a jihohin Ogun da Osun a ranar 10 ga watan Nuwamba da muke ciki.

Ya ce an ja hankalin rundunar ‘yan sanda ta kasa da sauran jami’an tsaro kan al’amarin kuma sun fara bincike.