On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

An Kama 'Dan Bindiga Mai Lakabin Sabon Jini Da Zargin Kisan Jami'in Dan Sanda A Jihar Katsina

Anyi nasarar kama, wani dan bindiga mai suna Sa’idu Yaro wanda aka fi sani da Sabon Jini mai shekaru 30, wanda ake zargin yana da hannu wajen kashe ACP Aminu Umar, Kwamandan ’Yan sandan Dutsinma na Jihar Katsina.

A ranar 5 ga watan Yuli ne ‘yan bindiga suka yiwa marigayi ACP Umar kwanton bauna suka kashe shi, a lokacin da yake jagorantar tawagar sintiri a aikin da aka saba yi na kawar da ‘yan ta’adda a yankin.

Rundunar ‘yan sandan dake sintiri ta samu rashin galaba a hannun ‘yan bindigar a wani kazamin artabu da suka yi da bindiga wanda a karshe ya yi sanadin mutuwarsa da  wani jami’in.

Mai magana da yawun ‘yan sanda a Katsina, ASP Aliyu Abubakar-Sadiq,  ya shaidawa manema labarai a cewa, an kama wanda ake zargin Sa’idu Yaro wanda aka fi sani da Sabon Jini a ranar 30 ga watan Agusta.