On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

An Kama Lalatacciyar Fulawa Sama Da Buhu 400 A Kano

HON. BAFFA BABBA

Hukumar Kare Hakkin Masu Siyen Kayayyaki ta jihar Kano, ta Dakume wasu Buhunan Filawa 487 data lalace ta milyoyin naira a jihar nan.

Mukaddashin Shugaban Hukumar, Alhaji Baffa Babba Dan Agundi ne ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa da Kakakin Hukumar Musbahu Yakasaio ya fitar a yau, Yace an kama Lalatacciyar Filawar ne a ranar Lahadi, biyo bayan wani sumame da suka kai wani wurin ajiyar kaya dake Kasuwar Dawanau.

Da yake tabbatar da lalacewar Filawar bayan gwajin samfurinta da aka yi, Baffa Babba Dan Agundi, ya kara da cewa Hukumar ta kama Lemukan sha wadanda suka lalace a kasuwar Abubakar  Rimi  da aka fi sani da Sabon gari dake nan kano.

Yace tuni aka kwashe kayayyakin da aka kama zuwa wurin ajiyar kaya na hukumar, Sannan kuma yayi  kira  ga  jama’a da su rika bawa  hukumar bayanai masu amfani wadanda zasu temaka mata wajen gudanar da aikinta.