On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

An Kama Mayakan Boko Haram Da Suka Shirin Kai Hari Gidan Atiku

ATIKU

An cafke wasu mutane hudu da ake zargin mayakan Boko Haram ne a birnin Yola na jihar Adamawa, lokacin da suke yunkurin kai harin Bam gidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar dake birnin na Yola.

Daya daga cikin wadanda ake zargin  mai suna Jibrila Mohammed mai shekara 29 a duniya,wanda  ya tabbatar da cewar  shi Dan Boko Haram ne, an  kama shi ne a kofar shiga  gidan Atiku Abubakar, lokacin da yake  kokarin kai harin da kimanin karfe  9  na daren  shekaran jiya.

Sanarwar da ofishin yada  labaran  jam’iyyar  PDP ya fitar, Ta  baiyana  cewar bayan kama matashin,an kuma sake  damke  wasu mutane  ukku da suke  tare  dashi.

Sanarwar  ta baiyana  cewar  an mika mutanen da ake zargi  hannun sojoji,sannan kuma sun fadawa  jami’an yansanda cewar,  maharani  sun yi niyyar  kai kan wasu kungiyoyi  dake aiki da Atiku Abubakar  da kuma wasu muhimman wurare a birnin na Yola.