On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Kama Tsohon Soja Dake Safarar Makamai Ga ‘Yan Ta’adda A Arewa Maso Yammacin Najeriya

Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta ce ta kama wani tsohon soja kuma kasurgumin dan fashin daji dake safarar makamai ga ‘yan bindiga a kan hanyarsa ta shiga jihar.

An kama dan fashin mai suna Sa’idu Lawal da bidiga AK-47 guda daya da AK-49, daya da harsasai masu tarin yawa

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta jihar SP Mohammed Shehu ya sanya wa hannu, ta ce dan fashin ya yi kaurin suna wajen aikata fashi da makami, da garkuwa da mutane, da safarar makamai da sauran laifukan da ke kawo cikas ga zaman lafiyar jihar da makwabtanta.

Sanarwar ta ce rundunarta mai yaki da aikata muggan laifuka ne ta kama dan Fashin mai shekara 41, wanda tsohon sojan Najeriya ne da ya taba aiki da bataliya ta 73 da ke Barikin soji ta Janguza a Kano.

An kama tsohon sojan ne a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a hanyarsa ta zuwa Zamfara lokacin da jami'an tsaro suka tsare motarsa domin gudanar da bincike, inda kuma nan take aka kama shi bayan samnunsa da makamai.

Dan fashin yace ya dauko makaman ne daga karamar hukumar Loko a jihar Nasarawa zuwa ga wani abokin huldarsa mai suna Dogo Hamza da ke kauyen Bacha a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Sa’idu Lawal ya kuma ce ya saba kai irin wadannan makamai ga kwastomominsa a jihohin Kaduna, da Katsina, da Niger da kuma Jihar Kebbi.