On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Kama Wani Magidanci Bisa Zargin Halaka Matar sa akan Abinci

'Yan sanda a Jihar Nasarawa sun kama wani mutum mai suna Musbawu Amodu mai shekaru 30 bisa zargin dukan matarsa har ta mutu bayan wata takaddama da ta shafi abinci.

Kakakin Rundunar 'Yan Sandan jihar, SP Ramhan Nansel, ya ce lamarin ya faru ne a Unguwar Yahaya da ke garin Agyaragu a Karamar Hukumar Obi, inda aka kai rahoton cewa mutumin ya lakada wa matarsa mai shekaru 20 duka har ta mutu.

Ya ce bayan samun rahoton, jami'an 'yan sanda sun garzaya wurin, inda suka kai gawar mamaciyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami'ar Tarayya da ke Lafiya domin bincike, sannan suka kama wanda ake zargin, wanda ya amsa cewa ya aikata hakan ne cikin fushi bayan matarsa ta ki dafa masa abinci.

SP Nansel ya ce ma'auratan sun shafe shekaru shida da aure kuma sun bar 'ya'ya biyu. Ya kara da cewa Kwamishinan 'Yan Sandan jihar, Shetima Mohammed, ya ba da umarnin mika shari'ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) domin gudanar da cikakken bincike, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thunder storm

    High: 33°C | Low: 23°C