On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An 'Karawa Najeriya Kwana 2 Domin Ta Kwashe Alhazanta Na Bana

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Saudiyya ta tsawaita izinin saukar jirage daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Yuli.

Hukumar aikin haji ta kasa NAHCON itace ta tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktar hulda da  jama'a da yada labarai Fatima Sanda Usara ta fitar a Abuja.

Tace  tsawaita wa’adin ya zama wajibi sakamakon soke  tashi da saukar jiragen sama da dama da akayi a baya.

Ta ce daga ranar 10 zuwa 13 ga watan Yuni an soke tashin jirage 9.

Hakan, a cewarta, ya samo asali ne saboda wasu dalilai da suka hada da gazawar wasu hukumomin alhazai na Jihohi wajen ba da kudin guziri  ga mahajjata da  rashin isassun kudade domin  biza da kuma rashin samun sakamakon gwajin cutar Corona