On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

An Karrama Wani Baturen 'Yan Sanda A Kano Saboda Yaki Karbar Cin Hancin Dala Dubu 200

ABOKIN KOWA DAN SANDA

Sufeton Rundunar ‘Yansanda ta kasa, Usman Alkali Baba Ya karrama Baturen ‘Yansanda na Karamar Hukumar Nasarawa dake nan jihar Kano, SP Daniel Itse Amah, sakamakon yadda yaki karbar cin Hancin Dala Dubu 200 da aka yi yunkurin bashi kan wata tuhuma ta zargin aikata lefin fashi da Makami.

An bawa baturen Yansandan Takardar shaidar Karramawa  ta musamman daga  hannun sufeton yansandan na kasa, Rahotanni sun baiyana cewa  zargin aikata lefin fashi da makamin ya shafi  wani Lauya ne da kuma wasu jami’an ‘yansanda.

Ta cikin wata wasikar yabo, An jinjinawa  mister Amah  bisa  yayi amfani da kwarewarsa  wajen jagorantar  cafke  Lauyan mai suna Ali Zaki da kuma wasu Jami’an ‘yansanda.

Tuni dai aka mika  tuhumar zuwa ga shalkwatar rundunar yansanda ta kasa dake Abuja, sakamakon umarnin da sufeton yansanda na kasa ya bayar, kamar yadda  jami’in hulda da jama’a na rundunar yansanda ta kasa Olomuyiwa Adejobi    ya baiyana.