On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Kori Karar Jam'iyyar PDP A Kotun Koli Kan Zaben Gwamnan Jihar Nasarawa

Kotun koli ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna David Umbugadu na jam’iyyar PDP ya shigar kan nasarar gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a zaben 2023.

Kwamitin alkalan a cikin hukuncin da suka yanke sun kori karar saboda rashin cancanta.

A ranar 2 ga Oktoba na 2023, kotun sauraron kararrakin zabe da ke Lafiya ta soke nasarar Gwamna Sule tare da bayyana David Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaben. 

Gwamna Sule da jam’iyyar APC sun nemi soke hukuncin inda suka daukaka kara kan hukuncin da kotun ta yanke. 

Kotun daukaka kara a hukuncin da ta yanke a ranar 23 ga watan Nuwamba, ta caccaki hukuncin kotun tare da tabbatar da zaben Sule a matsayin gwamna.