On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Kori Wasu Jami'an Hukumar Shige Da Fice 8 Saboda Karbar Na Goro

Hukumar shige da fice ta kasa ta baiyana cewar,Jami’anta kimanin 80 ne suka fuskanci shari’a gaban kotu saboda karbar Na goro, a lokacin da suke bada fasfo ko sabunta shi ga masu bukata.

Jami’in hulda da jama’a  na hukumar, Tony Akuneme,  shi ne  ya  tabbatar da haka ga manema labarai a ranar Lahadi, Ya kuma ce an kori wasu  guda  takwas  saboda  samunsu da aikata  lefuka daban daban a shekarar data  gabata.

Ya kara da cewar matakan ladabtawar da hukumar ke dauka,wani bangare ne  na kokarin kawo  gyara  da  sauye-sauye  a  hukumar shige da fice  ta kasa, karkashin mukaddashin shugaban hukumar Isah Jere.

Bugu da kari  ya  ce, Shugaban hukumar  ya ci alwashin  hukunta duk wani jami’in shige da fice da aka samu  da yunkurin yiwa  aiyukan hukumar  zagon kasa.