On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

An Nemi Aiwatar Da Sabon Albashin Sojoji

Tsofaffin sojojin Najeriya sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta fara aiwatar da mafi ƙarancin albashin naira dubu 250 da aka amince da shi ga jami'an sojin da ke aiki.

Sun bayyana hakan ne yayin wani taron bitar da suka gudanar a Abuja, inda suka ce Majalisar Dokoki ta amince da sabon tsarin albashin, kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu a dokar, sai dai har yanzu ba a fara aiwatar da ita ba.

Tsofaffin sojojin sun bayyana  rashin jin daɗinsu kan jinkirin, suna mai cewa an yi wannan gyaran albashi ne bayan wani bincike ya bayyana cewa sojojin Najeriya na daga cikin waɗanda ke karɓar mafi ƙarancin albashi a nahiyar Afirka.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 33°C | Low: 23°C