On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Sake Kammala Ganawa Tsakanin ASUU Da Gwamnatin Taraiyya Batare Da Cimma Matsaya Ba

ASUU DA WAKILAN GWAMNATIN TARAIYYA

An kammala Ganawar da aka sake yi tsakanin wakilan gwamnatin taraiyya da Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU batare da cimma wata matsaya ba.

Dukkanin wani  fata na  ganin an warware matsalolin da suka  haddasa  tafiya dogon yajin aiki da malaman jami’oin keyi, a zaman da suka yi da kwamitin da gwamnatin taraiyya ta kafa a karkashin Farfesa Nimi Brigss, a zaman da suka yi a jami’ar Kasa dake Abuja, ya karkare  batare  da samun  bakin zaren  ba.

Wani  mamba a cikin  kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU, Wanda ya nemi manema Labarai su sakaye sunansa, Yace  kwamitin farfesa  Brigs  bai zo masu da wani sabon tayi ba a yayin zaman da suka kwashe tsawon sa’oi ukku suna yi a tsakaninsu.

Yace  kwamitin ya roki Malaman ne kawai dasu janyen yajin aikin da suke yi , bisa alkawarin cewa  za’a shigar da dukkanin bukatunsu a cikin kunshin kasafin kudi na shekara mai zuwa.