On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Sake Samun Hatsarin Jirgin Ruwa A Jihar Adamawa Dake Najeriya

Ana fargabar mutane da dama  sun mutu a karamar hukumar Fufore ta jihar Adamawa, a ranar Litinin, yayin da wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji ya kife.

Babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa, Dr. Mohammed Suleiman, ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce  ya faru ne da rana kuma ana ci gaba da aikin ceto.

Wannan Iftila’I na zuwa ne  sa’o’i 48 bayan da mutane takwas suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Yola ta Kudu, yayinda  akalla mutane 24 suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale a jihar Neja ranar Lahadi.

Mahmud, wani masunci a yankin da ke cikin masu aikin ceto, ya shaidawa manema labarai cewa, za a iya hana aukuwar al’amarin idan fasinjojin sun yi amfani da rigar kariya  tare da aiwatar da wasu matakai na  kariya.